Mark 3

1Wani lokaci, da ya sāke shiga majamiʼa, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. 2Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci. 3Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”

4Sai Yesu ya tambaye su, ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci: a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.

5Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka,” sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 6Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hirudus yadda za su kashe Yesu.

Taron Jamaʼa Ya Bi Yesu

7Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi. 8Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi. 9Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi. 10Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi. 11Duk saʼad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.” 12Amma yakan tsauta musu, kada su shaida ko wane ne shi.

Naɗin Manzanni Sha Biyu

13Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa. 14Ya naɗa sha biyu-ya kira su manzanni
Waɗansu rubuce rubucen hannu ba su da kira su manzanni.
— don su kasance tare da shi, domin kuma yǎ aike su yin waʼazi,
15don kuma su sami ikon fitar da aljanu. 16Ga sha biyun da ya naɗa: Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus); 17Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗanʼuwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, ʼYaʼyan Tsawa); 18Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot, 19da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

Yesu da Beʼelzebub

20Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba. 21Da ʼyanʼuwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.”

22Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Beʼelzebub
Girik Beʼezebowul ko Beʼelzebowul
! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

23Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai, ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan? 24In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba. 25In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba. 26In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan. 27Hakika, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yǎ kwashe dukiyarsa, sai bayan ya ɗaure mai ƙarfin, saʼan nan zai iya yin fashin gidansa. 28Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi. 29Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”

30Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”

Mahaifiyar Yesu da ʼYanʼuwansa

31Sai mahaifiyar Yesu tare da ʼyanʼuwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yǎ kira shi. 32Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ʼyanʼuwanka suna waje, suna nemanka.”

33Ya yi tambaya, ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ʼyanʼuwana?”

34Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga mahaifiyata da ʼyanʼuwana! 35Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗanʼuwana, da ʼyarʼuwata, da kuma mahaifiyata.”

Copyright information for HauSRK